30 Janairu 2022 - 17:07
​Nigeriya: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda 3, Da Fararen Hula 18 A kasar A Makon da Ya Gabata

Akalla mutane 21 aka kashe a makon da ya gabata a tarayyar Najeriya, wato daga ranar 23-29 ga watan Jeneru mai karewa. Jaridar Premium times ta kara da cewa mutane 3 daga cikin wadanda aka kashen jami’an ‘yansanda ne, a yayinsa sauran kuma fararen hula ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Labarin ya kara da cewa idan an hada da mutane 486 wadanda aka kashe a makonni ukku na watan Jeneru na wannan shekarar, wato 486 adadin zai kama 507. Kuma mutane 21 da aka kashe a makon da ya gabata sun fito ne daga shiyar Arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin kasar.

Babu labarin ko akwai wadanda aka kashe a sauran shiyoyin 4. A makon da ya gabata dai an kashe mutane 9 a Zamfara, ‘yansanda 2 a Jigawa, Mutane 5 a jihar Ogun sai kuma 5 a Osun.

342/